CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI A duniyar zamani da ake ciki yau, Content Creation ya zama hanya mafi sauki da tasiri wajen isar da ilimi, nishaɗi, da kuma samun kuɗi ta yanar gizo. Abinda ake nufi da Content Creation shi ne kirkirar abubuwan da mutane zasu iya karantawa, kallo ko sauraro ta kafafen intanet. Misalai mafi shahara sun haɗa da Blogging, YouTube, da kuma Substack. Kowanne daga cikinsu yana da tsarin aikinsa, ribarsa, da kuma kalubale. 1. BLOGGING Ma’anarsa Blogging shine rubutun kasidu, labarai ko bayani a shafin yanar gizo (website/blog). Mutane da dama suna amfani da blogs domin rubuta ra’ayoyinsu, bayar da ilimi, ko tallata kayayyaki. Amfaninsa Bayar da ilimi: Rubutu na iya taimakawa wajen ilmantar da jama’a akan batutuwa daban-daban. Samun kuɗi: Ana iya saka Google AdSense, tallace-tallace, da affiliate marketing domin samun kuɗi. Gina suna: Blogging yana taimaka wa mutum ya zama mashahuri a fannin da yake rubutu. KALUBALE Bukatar h...
Comments