CYBERSECURITY= KARE KANKA DAGA HACKERS
Cybersecurity – Yadda Zaka Kare Kanka Daga Hackers
MENENE CYBERSECURITY?
Cybersecurity kariya ce da ake ɗauka domin kiyaye na’urori kamar waya, kwamfuta da tablet, da kuma bayanai irin su passwords da bayanan banki daga barazanar masu kutse (hackers).
HANYOYIN DA HACKERS KE AMFANI DA SU
1. Phishing – aika fake email ko links domin yaudarar mutum ya ba da sirrinsa.
2. Malware/Virus – shigar da apps ko software masu cutarwa a na’ura.
3. Weak Password – amfani da kalmar sirri mai sauƙin hango ko zato.
4. Public Wi-Fi Attack – satar bayanan masu amfani da mara tsaro Wi-Fi.
5. Social Engineering – amfani da dabarun yaudara wajen samun bayanai kai tsaye daga mutum.
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS
1. Karfafa Password
Yi amfani da kalmar sirri mai tsawo wadda ta ƙunshi haruffa, lambobi da alamu. Kada ka yi amfani da password ɗaya a duk asusun ka. Amfani da Password Manager zai taimaka wajen adana su.
2. Two-Factor Authentication (2FA)
Kunna 2FA a duk asusun ka na intanet kamar Facebook, Gmail da Bank apps. Wannan zai ƙara matakin tsaro koda hacker ya san password ɗinka.
3. Sabunta Software
Rikayin updating na system da apps domin sabbin updates yawanci suna gyara tsaro da magance barazanar zamani.
4. Ka Guji Fake Links da Emails
Kada ka danna duk wani link ko email da aka turo maka sai ka tabbatar daga sahihin tushe ya fito.
5. Amfani da Antivirus da VPN
Saya antivirus mai ƙarfi domin kare na’urar ka daga cututtuka. Idan kana amfani da Wi-Fi na jama’a ka yi amfani da VPN domin kare sirrinka.
6. Yin Backup na Bayanai
A rika yin backup na bayanai a cloud kamar Google Drive ko iCloud ko kuma external storage domin samun kariya idan na’urar ta lalace ko aka rasa bayanai.
7. Tsaron Social Media
Kada a bayyana duk wani bayani mai zurfi a Facebook ko Instagram. Ka tabbatar da settings ɗinka na privacy sun kasance masu tsauri.
8. Koyi Gane Yaudara (Scam)
Kada ka yarda da duk wani ya ce zai baka kuɗi cikin sauƙi ko ya nemi a aika masa da kuɗi kafin wani al’amari. Idan ya yi kama da yaudara, to yaudara ne.
KAMMALAWA
Cybersecurity ba abu ne da mutum ya yi sau ɗaya ya huta ba. Tsaro na yanar gizo dole ne a riƙa kula da shi kullum domin kare kai daga hackers. Yin hakan zai kare bayanai, kuɗi, da rayuwa gaba ɗaya daga barazana.
Follow my Facebook account for more information about science and technology
https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL

Comments