FACEBOOK MONETIZATION part2

Dan Turaki Tech FACEBOOK MONETIZATION part2

hanyoyi da mutum zai bi domin kiyaye sharuddan da kan hana Facebook monetization

1. Guji Satar Abun Wani (Copyrighted Content)
- Ka kirkiro content naka (bidiyo, hoto, rubutu).
- Kada ka ɗora fina-finai, wakoki, ko bidiyon wani ba tare da izini ba.
- Idan zaka yi amfani da abu na wani, *ka tabbatar da izini ko ka fadi sunansa* (credit).

2. Kiyaye Dokokin Facebook (Community Standards)
Guji:
- Cin mutunci, batsa, tsiraici
- Ƙiyayya bisa addini, ƙabila, ko launin fata
- Faɗin ƙarya ko fake news
- Bidiyon da ke da tashin hankali ko raunuka

3. Cika Bayanan Page ko Profile ɗinka
- Saka sunan da ya dace
- Sanya profile picture, cover photo
- Rubuta bio da contact info
- Kada ka yi amfani da sunan da ya saba doka (misali: “Facebook Giveaway Page”)

4. Guji Fake Engagement
- Kada ka siyo followers, likes ko views
- Kada ka yi amfani da bots ko apps masu karya doka
- Ka gina audience ɗinka ta halas

5. Inganta Content ɗinka
- Ka saka content da ke ilimantarwa, nishadantarwa ko fa’ida
- Ka karfafa comment, share da likes cikin halas
- Ka kasance da jadawalin posting (consistency)

6. Kar ka Saba Da Dokokin Monetization
- Ka karanta Facebook Partner Monetization Policies
- Ka dinga duba shafin (Monetization eligibility) a page settings ɗinka
- Idan Facebook ya baka warning, ka karanta ka gyara

7. Tsaftace Page ko Profile ɗinka:
- Share tsofaffin posts da ke iya karya doka
- Guji haɗin gwiwa da shafuka ko mutane masu matsala

 SHAWARA:
- Ka dinga duba Notifications daga Facebook
- Ka saka content ɗinka da *mutunci da manufa
- Ka duba Professional Dashboard domin ganin eligibility

Domin Samun rubututtuka masu amfani zaka iya ziyartar shafina 👇
https://danturakitech.blogspot.com

#dtarewadigitalhubs #danturakitech #monetization #share #earrings #SubscribeNow 

Dan Turaki Tech ✍️

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI