FACEBOOK MONETIZATION part4

FACEBOOK MONETIZATION part4

Wasu karin hanyoyi na samun kuɗi daga facebook 

1. Reels Play Bonus (via Professional Mode):
Wani shiri ne na gayyata (invite-only) inda Facebook ke biyan masu content bisa views da performance na Reels dinsu.

YADDA AKE SHIGA:
- Bude (Professional Mode) akan profile naka (ba Page ba).
- Yi posting Reels akai-akai
- Idan ka cancanta, zaka samu “You’ve been invited to Reels Play Bonus”

MISALI:
Idan Reels ɗinka ya kai 1 million views, Facebook zai baka 100 zuwa500 gwargwadon ƙasarka da engagement.

2. Facebook Ads Revenue Sharing:
Facebook yana saka talla (ads) a bidiyoyinka sannan ya raba kudin da kai (kamar YouTube).

Sharudda:
- 5,000 followers
- 60,000 watch minutes in 60 days
- 5+ active videos

MISALI:
Kana da bidiyo 10 da ke samun views, Facebook na saka ads a ciki, kuma zaka rika samun kuɗi daga su – kamar 2–10 per 1000 ad views.

3. Tools: Creator Studio & Meta Business Suite

Amfani:
- Dubawa ko kana eligible
- Bibiyar kuɗin da ka samu
- Shirya content calendar
- Testing (A/B test) don ganin irin content da ke jan hankalin mutane sosai

Misali:
- Ka yi post guda 2 daban, sai ka ga wanne yafi engagement
- Ka saka jadawalin Reels a kowane rana da lokaci

4. Appeal (Idan Facebook sun ƙi baka Monetization)

YADDA AKE:
- Je zuwa Professional Dashboard
- Idan monetization an ƙibaka, zaka ga "Request Review"
- Rubuta ƙwararan dalilai cewa ka gyara komai, kana bin doka yanzu

Misali:
- Idan Facebook ta hana ka Stars saboda copyright, ka cire duk abun da ya saba, sai ka roƙa a sake duba page ɗin

5. Yadda Ake Kara Followers da Watch Hours (Halal)*

HANYOYI:
- Reels masu jan hankali (30–60 sec)
- Bidiyo da nishadi, ilimi, ko labari
- Amfani da trending sounds
- Shiga comments da replying
- Yin live akai-akai

Misali:
- Ka yi video: “Yadda zaka daina kashe data a Android” – wannan yana jawo view da share sosai

Zamu cigaba 
Ku ziyarci shafina domin samun wasu bayanan kan ilimin technology
https://danturakitech.blogspot.com

#dtarewadigitalhubs #danturakitech #SubscribeNow #monetization #share #earrings #blogger 

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI