FACEBOOK MONETIZATION part1
FACEBOOK MONETIZATION part1
Insha Allah Yau zamu fara bayani kan Hanyoyi da mutum zai bi domin samun facebook monetization
FACEBOOK MONETIZATION
Hanyoyi da Sharuddan da Dole a Kiyaye
1. Menene Facebook Monetization?
Facebook Monetization wata dama ce da Facebook ke bayarwa ga masu ƙirƙirar abun ciki (content creators) domin su sami kuɗi ta hanyar abubuwan da suke wallafawa kamar bidiyo, rubuce-rubuce, hotuna, reels, da live streaming.
HANYOYIN MONETIZATION A FACEBOOK
1. In-stream ads
2. Stars
3. Subscriptions
4. Creator Storefront
Amma kafin su baka wannan damar ta samun kuɗi sai ka kiyaye wadan nan sharuddan:
1. Karya Dokar Facebook (Community Standards)
- Posting ɗin da ke dauke da:
- Batsa, tsiraici
- Kalaman ƙiyayya
- Cin mutunci ko fake news
- Ƙarfafa tashin hankali
2. Karya Dokar Monetization (Monetization Policies)
- Hakan ya haɗa da:
- Satar bidiyo ko hoton wani (copyright)
- Yin amfani da content ba tare da izini ba
- Reposting content ba tare da ƙirƙira sabo ba
3. Low Engagement ko Fake Followers
- Idan ka siyo followers ko likes
- Idan content ɗinka baya samun natural engagement (likes, comments, views)
4. Yawan Report daga mutane
- Idan mutane da yawa suna korafi (report) akan content ɗinka
5. Repeated Violations
- Idan account ɗinka ya saba doka fiye da sau ɗaya ko ya samu (restrictions)
6. Babu Cikakken Bayani a Page/Profile
- Idan kana da *fake name* ko babu cikakken bio, profile picture, da sauransu
7. Rashin Cika Sharuddan Tattalin Arziki (Eligibility Criteria)
- Misali:
- 5,000 followers ba su cika ba
- Watch time bai kai ba
- Page ba na ƙasa da Facebook ke biya ba (kamar Najeriya ba a yi da farko)
Zamu kawo yadda zaka kiyaye
Domin Samun rubututtuka masu amfani zaka iya ziyartar shafina
https://danturakitech.blogspot.com
#monetization #danturakitech #earrings #dtarewadigitalhubs #share
Comments