HANYOYIN DA ZAKA SAMU KUDI A OPAY

 HANYOYIN DA ZAKA SAMU KUDI A OPAY_part1


MENENE OPAY 


OPAY: wata manhaja ce ta hada-hadar kudi (mobile payment app) da ke ba masu amfani damar hadakar kudade. 


BABBAN AIKI NA OPAY

1. Aika da karɓar kuɗi (transfer)

2. Biyan kuɗin waya, data, wuta, DSTV da sauransu

3. Ajiya da samun riba (ta hanyar Owealth)

4. Sayar da airtime/data ga mutane

5. Aikin POS (idan ka zama wakili)


AMFANINTA

- Mai sauƙin amfani

- Ba ya caji kudi sosai

- Yana aiki cikin sauri

- Na da cikakken tsaro

- Akwai tallafi 24/7


Opay na da amfani ga kowa: dalibai, masu sana’a, da ’yan kasuwa.


HANYOYIN SAMUN KUDIN 


1. Yin Aikin POS (Agent)*

Wannan ita ce hanya mafi shahara. Idan ka zama wakilin Opay (POS agent), zaka rika:

- Karɓar kuɗi daga mutane (cash deposit)

- Cire musu kuɗi (withdrawal)

- Biya kudin wutar lantarki, ruwa, DSTV, da sauransu

- Canja kuɗi daga account ɗin su


Ribarka: Kana samun ƙaramin kaso (commission) daga kowanne ma’amala da kayi da abokan kasuwancin ka.


2. Referral (Gayyatar mutane)

Opay na bada lada idan ka gayyato wani ya bude account ta link ɗinka.  

- Idan mutum ya yi rajista kuma ya fara amfani da app ɗin, zaka iya samun kuɗi har N500 ko fiye bisa ga sharuɗɗansu.


3. Aikace-aikacen Kudi (Savings & Investment)

- Opay na da Owealth, inda zaka iya ajiye kuɗi kuma ya rika haifar maka riba (interest).

- Ana iya samun kaso na ,(15%) a shekara (ya danganta da adadin da ka ajiye).


Next

#dtarewadigitalhubs #earrings OPay #share 


Ɗan Turaki ✍️

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI