HANYOYIN DA ZAKA SAMU KUƊI A OPAY _part3
HANYOYIN DA ZAKA SAMU KUDI A OPAY_part3
Samun kuɗi da Opay ta hanyar POS Agent da Referral Program
1. Hanya ta Farko: Opay POS Agent
Wannan na nufin ka zama wakilin Opay da ke amfani da POS machine don:
- Karɓar kuɗi daga abokan ciniki (deposit)
- Fitar da kuɗi (withdrawal)
- Biyan wuta, data, DSTV, ruwa da sauransu
YADDA ZAKA FARA:
1. Sauke Opay App daga Play Store
2. Yi rajista da cikakken bayani
3. Ka je shafin “Merchant Application” Cika form don neman POS
4. Bayan sun tantance ka, za su baka POS (wani lokacin kyauta, wani lokacin ka biya)
YADDA ZAKA SAMU KUƊI:
- Opay na baka commission akan kowace ma’amala da kayi, misali:
- Withdrawal na N1000, zaka iya samu N10+
- Bill payment na N10,000 zaka samu wani abu.
- Idan kana da yawan abokan ciniki kullum, zaka iya samu dubu dubu a rana
ABIN LURA
- Ba sai kana da shago ba, zaka iya yin aiki da POS ko a titi
- Za ka iya ba wasu POS, su rika aiki a ƙarƙashinka.
2. Hanya ta Biyu: Opay Referral Program
Referral na nufin gayyatar mutane su bude account na Opay ta hanyar link ɗinka ko code.
Yadda Zaka Yi:
1. Shiga Opay app
2. Je zuwa “Referral” ko “Invite & Earn” section
3. Sami link ɗinka ko referral code
4. Tura link/code ɗin ga abokai, dangi, a WhatsApp, Facebook, da sauransu
5. Idan sun bude account kuma sun fara amfani da shi (kamar suyi transfer ko airtime), zaka sami kuɗi (misali N500 ko fiye)
SHAWARWARI:
- Ka rubuta bayanin yadda ake rajista ka tura shi tare da link
- Ka gaya musu su fara amfani da app ɗin (ba rajista kawai ba)
A Taƙaice:
Hanya / Yadda ake samun kuɗi
1. POS Agent / Commission daga withdrawals, transfers, bill payments
2. Referral / Kuɗi daga kowane sabon mutum da ka gayyata kuma ya yi amfani da app
Zamu kawo sauran Insha Allah
Ku ziyarci shafina domin samun wasu bayanan 👇
https://danturakitech.blogspot.com
#opay #danturakitech #dtarewadigitalhubs #share #SubscribeNow OPay
Dan Turaki Tech ✍️
Comments