MENENE CODING DA PROGRAMMING

 

MENENE CODING?


Coding shi ne rubuta umarnin (instructions) da kwamfuta za ta fahimta.


Kamar yadda kake rubuta wasiƙa da Hausa, haka ma Coding rubutun ne amma a cikin harshen kwamfuta (Programming Language).


Coding shi ne ainihin aikin da ake yi don ƙirƙirar software, websites, apps, ko kuma shirye-shirye daban-daban.


Misali:


print("Sannu Duniya")


Wannan rubutun a Python zai sa kwamfuta ta nuna "Sannu Duniya" a screen.


MENENE PROGRAMMING?


Programming ya fi Coding girma.


Shi ne tsarin tsara, tunani, rubutawa, gyarawa da kuma kula da shirin kwamfuta.


Yana ɗauke da matakai kamar planning (tsara), design (ƙirƙira tsarin), coding (rubutun code), testing (gwaji), da maintenance (gyara/ingantawa).



A TAƘAICE:


Coding = Rubuta code kawai.


Programming = Dukkan tsarin ƙirƙirar software daga farko har ƙarshe.


 BAMBANCI TSAKANIN CODING DA PROGRAMMING:

Sifa Coding Programming


Ma’anarsa Rubuta code da harshen kwamfuta Ƙirƙira tsarin cikakken shiri (planning + coding + testing)

Hanya Rubutun kai tsaye Tunani + tsara + coding + gwaji

Misali Kamar rubuta kalma ɗaya da Hausa Kamar rubuta littafi gaba ɗaya da Hausa

Aiki Ƙananan matakai na software Babban tsarin ƙirƙira software


MUHIMMANCIN CODING DA PROGRAMMING

1. Ƙirƙirar apps (WhatsApp, Facebook, TikTok).

2. Gina websites (Google, YouTube, Blog ɗinka).

3. Ƙirƙirar games.

4. Aikin AI/Robotics.

5. Samun ayyukan nesa (remote jobs) da kuɗi a duniya.


MISALAN HARSHEN CODING/PROGRAMMING


-Python (mai sauƙi, ana amfani da shi wajen AI, Data, Web).

-JavaScript (ana amfani da shi wajen websites da apps).

-Java, C++, C# (ana amfani da su wajen games, software).

-HTML & CSS (ana amfani da su wajen websites).


IDAN KANA SON FARAWA

1. Ka zabi harshen farko mai sauƙi (Python ko JavaScript).

2. Ka yi amfani da free platforms kamar:

W3Schools

FreeCodeCamp

Codecademy


3. Ka fara da ƙananan projects kamar Calculator, To-do list, ko Blog page.


 A TAƘAICE:


Coding = Rubutun harshen kwamfuta.

Programming = Tsarin duk aikin ƙirƙira shirin kwamfuta.


Kuyi Following din account page din mu na facebook domin samun wasu ingantattun ilmai 👇

https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL

Comments

Anonymous said…
gaskiya muna godiya sosai Allah ya kara basira amma a Ina yakamata kasamu wannan website don koyon wannan coding din

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI