MENENE HAVE A LONG TEAM VISION
HAVE A LONG-TERM VISION na nufin ka kasance da hangen nesa da burin dogon lokaci a rayuwarka, kasuwanci, ko karatu.
1. MENENE LONG-TERM VISION?
Long-term vision shine burin da kake da shi wanda zai ɗauki lokaci kafin ya cika — watanni ko shekaru. Yana duba inda kake son kai kanka ko aikinka a nan gaba.
2. AMFANIN SAMUN HANGEN NESA (LONG-TERM VISION):
- Yana ba ka shiri: Ka san inda kake nufa, hakan yana taimaka maka wajen shirya tsari.
- Yana kare ka daga rudani: Ba za ka rika bin abubuwan da ba su da amfani ba.
- Yana motsa ka: Idan kana da buri na dogon lokaci, hakan yana sa ka dage a yau.
- Yana kawo nasara: Masu nasara da yawa suna da hangen nesa tun kafin su fara.
3. MISALAI:
- Idan kana karatu, long-term vision ɗinka na iya kasancewa “na zama kwararren injiniya cikin shekaru 5.”
- A kasuwanci, zaka ce “na mallaki kamfani da ma’aikata 50 cikin shekaru 10.”
- A social media, zaka ce “na zama mai tasiri da followers 1M cikin shekaru 3.”
4. YADDA AKE TSARA LONG-TERM VISION:
- Sanin abin da kake so a rayuwa
- Rubuta burinka da tsari
- Raba burin zuwa matakai (goals)
- Aiki da juriya akai-akai
Kammalawa:
HAVING A LONG-TERM VISION yana nufin rayuwa da buri mai ma’ana. Ka san inda zaka, ka dage da aiki akansa, kuma kada ka bari matsalolin yau su hana ka ganin gobe.
Ka fara yau da tambaya: “Ina nake so in ga kaina nan da shekara 5 zuwa 10?”
Flowdiary 📽️
Dan Turaki Tech ✍️

Comments