MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KASANI KAFIN KA SAYI COMPUTER
Ga muhimman abubuwan da mutum ya kamata ya sani kafin ya sayi computer (laptop ko desktop):
1. Dalilin Amfani da Computer
Ka fara tantance me za ka yi da ita:
-Idan don karatu, browsing da rubutu ne ƙaramin specification zai yi.
-Idan don design, programming, editing, ko gaming ne sai ka ɗauki mai ƙarfi sosai.
2. Processor (CPU)
Shi ne zuciyar computer, yana nuna yadda za ta yi sauri.
Akwai nau’o’i:
-Intel (i3, i5, i7, i9)
-AMD Ryzen (Ryzen 3, Ryzen 5, Ryzen 7, Ryzen 9)
KAƘKAUSAR SHAWARA:
-Don amfani na yau da kullum Core i3 / Ryzen 3.
--Don aiki mai nauyi (video editing, programming, graphics) Core i5/i7 ko Ryzen 5/7.
-Don gaming ko manyan ayyuka i7/i9 ko Ryzen 7/9.
3. RAM (Memory)
-RAM tana taimaka wajen gudu da aiki da yawa lokaci ɗaya.
-4GB kananan aiki kawai.
-8GB ya fi dacewa ga ɗalibi, office, browsing.
-16GB ko sama editing, design, coding, gaming.
4. Storage (Hard Drive)
-Nau’in HDD da SSD.
-HDD mai ɗaukar bayanai da yawa amma baya da sauri.
-SSD yana da sauri sosai, amma ba ya ɗaukar bayanai da yawa.
SHAWARA:
-Idan za ka iya SSD 256GB+ ko kuma haɗin SSD + HDD.
5. Graphics (GPU)
-Idan kana so ka yi gaming, design, editing ka duba wacce take da Dedicated Graphics (NVIDIA/AMD).
-Idan don word, browsing, online class Integrated Graphics ya isa.
6. Battery Life (idan Laptop)
-Idan kana yawan fita da shi ka zaɓi wanda ke da awa 5 zuwa 8 aƙalla.
-Idan ba za ka yawan fita da shi ba komai zai yi.
7. Screen Size & Resolution
- 14" – 15.6" ya fi dacewa (balance tsakanin girma da ɗauka).
-Idan don editing ka fi dacewa da Full HD (1080p) ko sama.
8. Ports & Connectivity
-Ka tabbatar tana da USB 3.0, HDMI, WiFi, Bluetooth, idan za ka yi amfani da su.
-Idan kana buƙatar Type-C ko Thunderbolt, ka duba kafin saye.
9. Operating System (OS)
-Windows yawanci ana amfani da shi sosai.
-MacOS (Apple) ga masu son Apple ecosystem.
-Linux ga programmers/tech.
10. Budget (Kuɗin Ka)
Ƙayyade iyakar kuɗin da kake da shi, sannan ka nemi mafi inganci a ciki.
TAKAITACCEN SHAWARA:
Idan kai ɗalibi ne ko don aikin yau da kullum:
Core i5, 8GB RAM, 256GB SSD, 15.6” Screen zai fi dacewa.
Idan kana sha’anin editing, coding, ko
graphics:
Core i7/Ryzen 7, 16GB RAM, Dedicated Graphics, 512GB SSD.
Ku tuntubi yallaɓai saheel domin samun computers masu inganci
https://www.facebook.com/salisuabdurrazaksaheel?mibextid=ZbWKwL
Please share 🙏 & FOLLOW MY FACEBOOK PAGE
https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL

Comments