OPERATING SYSTEM= ANDROID, IOS, WINDOWS

 

1. Android OS


Menene shi?

Android Operating System wani tsarin aiki ne da Google ta samar wanda ake amfani da shi a mafi yawan wayoyin salula (smartphones), tablets da wasu na’urori masu haɗi.


Amfani:


-Yana goyon bayan miliyoyin apps daga Google Play Store.

-Yana da sassauci sosai (open-source) wato ana iya gyara shi ta hanyoyi da dama.

-Yana aiki da na’urorin kamfanoni daban-daban kamar Samsung, Tecno, Infinix, Oppo, Xiaomi da sauransu.


2. iOS

Menene shi?

iOS shine tsarin aiki na Apple, wanda ake amfani da shi a iPhone, iPad, da iPod Touch.


AMFANI:

1. Tsaro mai ƙarfi sosai.

2. Yana da sauƙin amfani da ingantaccen tsari.

3. Ana samun apps daga Apple App Store kawai.

4. Yana aiki ne kawai a na’urorin Apple (ba kamar Android ba).


3. Windows OS


Menene shi?

Windows Operating System shine tsarin aiki da Microsoft ta ƙirƙira, kuma shine mafi yawan amfani a kwamfutoci (PC & Laptop).


AMFANI:

1. Yana goyon bayan shahararrun software kamar Microsoft Office, Adobe, AutoCAD da sauransu.

2. Ana amfani da shi wajen ofis, makaranta, kasuwanci, da kuma wasa (gaming).

3. Yana da nau’uka daban-daban (Windows 7, 8, 10, 11).

4. Kwatanta (Comparison)

5. Operating System Na’urorin da ake amfani da shi Ƙarfi Iyakancewa

6. Android Wayoyin salula, Tablets Yana da sassauci, apps da yawa, arha Tsaro bai kai iOS ba

7. iOS iPhone, iPad Tsaro mai ƙarfi, ingantaccen aiki Na’urori masu tsada, apps daga App Store kawai

8. Windows PC, Laptop Yana goyon bayan software da yawa, sauƙin amfani Ba 

9. ya aiki da wayoyi (sai PC), na iya yin slow idan ba a kula ba


Follow my Facebook page

https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL


Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI