THINK OUTSIDE THE BOX
THINK OUTSIDE THE BOX
"Think outside the box" na nufin tunani fiye da yadda aka saba, ko zuwa fiye da iyaka da kowa ke tunani. Wato ka daina yin tunani cikin ƙuntataccen hanya kamar kowa, ka buɗe tunaninka don kawo sabbin hanyoyi, mafita, ko dabaru da ba a saba dasu ba.
Misali:
- Idan kana kasuwanci kuma kowa yana amfani da flyers, sai kai ka ƙirƙiro app ko WhatsApp bot – wannan "thinking outside the box" ne.
- A makaranta, idan kowa yana karatu da littafi, kai ka fara amfani da video da audio summaries don sauƙaƙa fahimta.
ME YASA YAKE DA AMFANI GAREMU ?
1. Yana haifar da sabbin dabaru
2. Yana baka damar fita daban
3. Yana jawo hankalin mutane
4. Yana haifar da mafita a lokacin da sauran sun gagara
5. Yana taimakawa wajen cin gasa da fice a sana’a ko rayuwa
YADDA ZAKA FARA “THINKING OUTSIDE THE BOX”
- Tambayi kanka: “Me zai faru idan nayi haka daban?”
- Guji bin hanyar da kowa ke bi kawai saboda sunce haka ake
- Ka gwada sabbin dabaru koda ba kowa ya yarda da su ba
- Koyi daga wasu ƙasashe, al’umma ko masana daban
- Ka haɗa ilimi da kwarewa don ƙirƙirar sababbin mafita
THINKING OUTSIDE THE BOX NA BUƘATAR:
- Buɗaɗɗen tunani
- Rashin tsoro wajen gwadawa
- Yin abu daban da yadda aka saba
- Hangen nesa da hangen gaba
Ziyarci shafina domin samun ingantaccen ilimin fasaha
https://danturakitech.blogspot.com
#dtarewadigitalhubs #danturakitech #SubscribeNow Flowdiary #monetization #blogger #share #earrings
Comments