WIPES AWAY YOUR HINDRANCES


 

WIPE AWAY YOUR HINDRANCES 

Share Matsalolinka Ka Ci Gaba


Ma’anar Taken:

"Wipe away your hindrances" na nufin ka kawar da duk wani abu da ke hana ka ci gaba a rayuwa– ko na zuciya ne, ko na rayuwa, ko kuma matsaloli daga wajen wasu. Wato ka cire shinge, ka fitar da cikas, ka tunkari burinka ba tare da jinkiri ba.


ME AKE NUFI DA “HINDRANCES”?

Hindrances na iya zama:

- Tsoron fadi tashi (fear of failure)

- Rashin yarda da kanka (self-doubt)

- Surkullen mutane ko maganganu

- Rashin ilimi ko kwarewa

- Tashin hankali da damuwa (stress, trauma)

- Ƙuntatacciyar hanya ta tunani


YADDA ZA KA “WIPE AWAY” SU:


 1. Gane cikas ɗinka

– Ka tambayi kanka: Me nake tsoro? Me nake ta jinkirta? Me ke hana ni farawa?


 2. Sanya niyyar kawar da su

– Ka ce da kanka "Zan iya, kuma zan yi"– ka daina zargin kanka ko jiran kwarin gwiwar wasu.


 3. Ƙara ilimi da horo

– Idan rashin ilimi ne ke hana ka ci gaba, sai ka nema – karatu, training, ko mentorship.


4. Kuskure ba laifi ba ne

– Ka daina jin nauyin gwadawa. Idan ka faɗi, ka koyi darasi, ka gyara ka ci gaba.


 5. Ka ware kanka daga masu rage maka ƙima

– Wasu mutane kalamansu cikas ne. Ka rage yawan kusanci da su ko ka kauce musu.


MISALAI:


- Fatima na son fara YouTube amma tana jin kunyar magana. Ta fara daukar bidiyo a sirrince har sai ta saba. Yanzu tana da 10k subscribers.

  

- Umar yana tsoron fita kasuwa saboda ana ce masa ba zai iya ba. Ya share maganganu, ya fara da N1,000, yanzu yana jarin 100k 


FA’IDAR KAWAR DA CIKAS:

- Zaka samu kwanciyar hankali

- Zaka fara ayyukanka cikin kwarin gwiwa

- Zaka shiga sahun masu nasara

- Zaka zama abin koyi

- Rayuwarka zata samu sauyi da gamsuwa



A Taƙaice:


Matsala ----- Magani 

-Tsoron fara abu --- Ka fara da ƙaramin mataki |

-Rashin goyon baya ---- Ka zama mai goyon bayan kanka 

-Maganar mutane ---- Ka mayar da hankali kan burinka 

-Rashin ilimi ----Ka nemi sanin da kake buƙata 

- Jinkiri ---- Ka fara yau, koda ba cikakke ba 

"Kada cikas yahana ka, ka tashi ka share su. Rayuwa ta fi jiranka a gaba.”


Dan Turaki Tech ✍️

https://danturakitech.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI