AMFANIN GOOGLE BUSINESSES GA YAN KASUWA DA YADDA AKE BUDE SA
MENENE GOOGLE BUSINESS PROFILE DA AMFANIN SA GA ‘YAN KASUWA?
A duniyar zamani, yawancin mutane suna amfani da Google wajen neman kayayyaki da aiyuka kafin su yanke shawarar siye ko zuwa wani wuri. Wannan yasa Google ta ƙirƙiri wata hanya mai sauƙi wacce zata taimaka wa ‘yan kasuwa su bayyana a kan intanet. Wannan hanya ita ce Google Business Profile.
MENENE GOOGLE BUSINESS PROFILE?
Google Business Profile wata manhaja ce kyauta daga Google wacce take ba ka damar sanya kasuwancin ka a cikin Google Search da Google Maps. Da zarar ka saka kasuwancin ka, duk wanda ya yi bincike da ya shafi sana’arka zai iya ganin sunan kasuwancin ka, adireshinka, lambar waya, taswira, sa’o’in aiki, hotuna, da ma shawarwarin (reviews) daga kwastomomi.
Misali, idan wani ya rubuta “shagon waya a Kano”, Google zai nuna masa jerin shaguna tare da cikakken bayani. Idan ka saka kasuwancin ka a Google Business, zaka kasance cikin wannan jerin.
AMFANIN GOOGLE BUSINESS PROFILE
1. Bayyana kasuwanci a Google Search da Google Maps
– Wannan yana sa mutane su same ka cikin sauƙi duk inda suke.
2. Ƙara samun sababbin kwastomomi
– Duk wanda ya nemi irin kayanka ko aikinka zai iya gano kai cikin mintuna kaɗan.
3. Bayar da cikakken bayani ga kwastomomi
– Kana iya saka lambar waya, sa’o’in aiki, adireshi, hotuna, har da link ɗin website.
4. Karɓar reviews daga kwastomomi
– Reviews suna ƙara martabar kasuwanci saboda mutane sukan dogara da ra’ayin waɗanda suka riga sun gwada.
5. Taimakon nazari (Insights)
– Google zai baka rahoto akan yadda mutane suka gano kasuwancin ka, adadin mutanen da suka danna lambar waya ko suka shiga website ɗinka.
6. Kyauta ne gaba ɗaya
– Ba sai ka biya ko sisi ba domin amfani da wannan dama.
YADDA AKE BUƊE GOOGLE BUSINESS PROFILE (MATAKI-MATAKI)
1. Shiga shafin Google Business Profile
– Je zuwa: Https://business.google.com
2. Shiga da account ɗin Gmail ɗinka
– Idan baka da Gmail, sai ka fara buɗewa.
3. Saka sunan kasuwancin ka
– Rubuta cikakken suna yadda yake a wajen kasuwanci.
4. Zaɓi category (nau’in kasuwanci)
– Misali: Restaurant, Shagon waya, Masallaci, Hotel, da sauransu.
5. Saka adireshin kasuwanci
– Hakan zai taimaka kwastomomi su same ka ta Google Maps.
6. Ƙara bayanai masu amfani
– Lambar waya, adireshi, link ɗin website (idan kana da shi), da hotunan kasuwancin ka.
7. Tabbatar da kasuwanci (Verification)
– Google zai turo maka code ta waya ko ta wasiƙar gida domin tabbatarwa.
8. Fara amfani da shafin
– Bayan ka tabbatar, zaka iya sa hotuna, wallafa sabbin kayayyaki ko sabis, da karɓar reviews daga kwastomomi.
ATAKAICE
Google Business Profile hanya ce ta zamani da ba sai ka kashe kuɗi ba wacce zata taimaka maka wajen jawo sababbin kwastomomi, ƙara martaba, da bayyana kasuwancin ka a duk inda mutane suke neman kayayyaki a intanet. Idan kai ɗan kasuwa ne mai son ƙara darajar kasuwancin ka, to Google Business P
rofile na daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata ka fara amfani da su tun yanzu.
FOLLOW MY FACEBOOK PAGE FOR MORE INFO
https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL

Comments