GOOGLE FAMILY LINK TRACKER: Hanyar Kulawa da Yadda Yara ke Amfani da Wayar Android

 

Google Family Link Tracker: Hanyar Kulawa da Yadda Yara ke Amfani da Wayar Android


Gabatarwa


A wannan zamani, yara da matasa suna da sauƙin samun wayoyi da intanet. Wannan yana da alheri saboda yana taimaka musu wajen koyo da sadarwa, amma kuma yana iya zama barazana idan basu da kulawa. Don haka Google ya ƙirƙiro Family Link, wata manhaja da ke bawa iyaye damar sa ido, tsara lokaci, da kuma bibiyar inda yaransu suke.


A WANNAN RUBUTU, ZAMU KALLI:


1. Ma’anar Family Link.

2. Amfaninsa.

3. Illolinsa.

4. Matakan da iyaye za su bi wajen saita shi.


MENENE GOOGLE FAMILY LINK TRACKER?


Google Family Link wata app ce na iyaye (Parental Control App) da aka tsara domin taimaka musu wajen:


-Saita iyaka kan amfani da waya.

-Tabbatar da apps da yara ke saukewa.

-Kula da wurin da yaro yake a duk lokacin da yake da waya.

-Samar da rahoton amfani da waya.

-A takaice, Family Link yana aiki a matsayin Google tracker na yara.


AMFANIN GOOGLE FAMILY LINK


1. Kulawa da lokaci – Iyayen na iya saka lokacin amfani da waya, musamman lokacin kwana da karatu.

2. Bibiyar wurin yaro – Yana nuna inda yaro yake a taswira ta Google Maps.

3. Tantance apps – Duk app da yaro zai sauke sai iyaye sun amince.

4. Kulle waya daga nesa – Waya zata iya kullewa daga nisan kilomita koda iyaye ba kusa suke ba.

5. Rahoton amfani – Iyayen zasu ga tsawon lokacin da aka bata a WhatsApp, TikTok, ko sauran apps.


ILLOLI KO KALUBALE


-Zai iya jawo ƙuncin rai ga yara saboda suna jin kamar ba’a yarda da su.

-Yana buƙatar intanet (data/wi-fi) don ya yi aiki yadda ya kamata.

-Ba koyaushe yake bada sahihin location ba idan an kashe GPS ko intranet 


YADDA IYAYE ZASU SAITA GOOGLE FAMILY LINK

Ga matakan da za a bi daga farko har ƙarshe:


MATAKI NA 1: SAUKE APP ƊIN

-Iyayen su sauke Google Family Link for Parents daga Google Play Store ko App Store (idan iPhone ne).

-Yaro kuma ya sauke Google Family Link for Children & Teens.


Mataki na 2: Buɗe Account ɗin yaro

-Idan yaro bai da Gmail, iyaye su ƙirƙira masa sabon account.

-Idan yana da Gmail, za a haɗa shi da Family Link na iyaye.


MATAKI NA 3: HAƊA WAYOYI

-Iyayen zasu buɗe app ɗin Family Link a wayarsu.

-Za a tambaye su su saka account na yaron.

-Bayan haɗawa, iyaye suna da ikon kula da wayar yaron daga nesa.


MATAKI NA 4: SAITA DOKOKI

1. Sanya Screen Time Limit (misali awa 2 a rana).

2. Zaɓi lokacin da waya zata kulle da kanta (bedtime).

3. Tantance apps da yaro zai iya saukewa


MATAKI NA 5: KULAWA DA LOCATION

Iyayen za su iya duba wurin yaro a taswira (Google Maps) kai tsaye daga app ɗinsu.


KAMMALAWA


Google Family Link na daya daga cikin mafiya amfani ga iyaye a wannan zamani. Yana bada damar haɗa tarbiyya da tsaro, tare da tabbatar da cewa yara suna amfani da waya cikin tsari. Duk da cewa zai iya jawo musu jin takura, idan aka yi amfani da shi cikin hik

ima zai taimaka wajen kare su daga haɗarin da ke cikin intanet.


FOLLOW MY FACEBOOK PAGE 

https://www.facebook.com/profile.php?id=61579886394478&mibextid=ZbWKwL

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI