MENENE AMFANIN DO NOT DISTURB (DND) A WAYA DA YADDA AKE SAITA SHI


 

MENENE AMFANIN DO NOT DISTURB (DND) A WAYA DA YADDA AKE SAITA SHI


Do Not Disturb (DND) wani fasali ne da ake samu a cikin wayoyin zamani wanda ke nufin “Kada a Dame Ni”. An kirkiro shi ne domin bai wa mai waya damar samun natsuwa da kariya daga hayaniyar kiran waya ko saƙonni a lokutan da bai dace a dame shi ba.


AMFANIN DND A WAYA


1. Dakatar da Kiran Waya

Idan ka kunna DND, wayarka ba za ta yi kara ba idan wani ya kira ka, amma za ka ga kira a jere idan ka duba bayan daga baya.

2. Kare Bacci da Natsuwa

Yana taimaka maka ka huta cikin natsuwa, musamman da daddare ko a lokacin taro da aiki mai muhimmanci.

3. Toshe Sautin Saƙonni da Sanarwa

Ba za ka ji ƙarar SMS ko sanarwar apps ba, sai ka kashe DND.

4. Zaɓin Mutanen da za su iya Shiga Maka

Kana iya saita cewa iyali ko abokai na musamman su iya kiran ka duk da DND.

5. Rage Damuwa

Yana ba ka damar yin abu cikin natsuwa ba tare da hayaniyar wayar ka ba.


YADDA AKE SAITA DND A WAYA


A WAYAN ANDROID

1. Je zuwa Settings (Saituna).

2. Danna Sound & Vibration ko Notifications (ya danganta da samfurin waya).

3. Za ka ga Do Not Disturb, sannan ka kunna.

4. Kana iya saita jadawali misali daga 10 na dare zuwa 6 na safe.

5. Idan kana so, za ka iya zaɓar mutanen da za su iya kiran ka duk da cewa DND yana kunne.


Haka kuma, zaka iya samun sauri ta hanyar ja Notification bar ƙasa daga sama, sannan ka zaɓi Do Not Disturb daga cikin Quick Settings.


A WAYAN IPHONE (IOS)


1. Je zuwa Settings.

2. Bude Focus, sannan ka danna Do Not Disturb.

3. A nan zaka iya kunna shi kai tsaye ko ka sa jadawali.

4. Hakanan zaka iya zaɓar apps da mutanen da za su iya turawa maka sanarwa duk da cewa DND yana kunne.


Kuma zaka iya kunna shi cikin sauƙi ta hanyar buɗe Control Center sannan ka zaɓi Do Not Disturb.


TIPS NA AMFANI DA DND


LOKACIN BACCI: Saita jadawali na DND daga lokacin da kake shirin kwanciya har zuwa lokacin da kake tashi. Wannan zai hana hayaniyar kira da sanarwa tada ka a tsakiyar bacci.


LOKACIN AIKI: Idan kana karatu ko aiki mai muhimmanci, kunna DND domin ka mai da hankali ba tare da hayaniyar waya ba.


LOKACIN IBADA: Yana da amfani a lokacin sallah ko wata ibada, domin zai tsare kowane sauti na cikin wayar Ka .


KAMMALAWA

DND wata hanya ce da ke taimaka wa mai waya wajen samun hutu da nutsuwa. Idan aka yi amfani da shi yadda ya dace, zai taimaka wajen bacci cikin salama , aiki cikin natsuwa batare da sauti ba 

 

Kuyi follow na Facebook page din mu 

https://www.facebook.com/share/175ahJxb3F/

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI