MENENE CLOUD COMPUTING? KUMA YAYA YAKE SAUƘAƘA RAYUWARMU A ZAMANI?


 

MENENE CLOUD COMPUTING? KUMA YAYA YAKE SAUƘAƘA RAYUWARMU A ZAMANI?


MENENE CLOUD COMPUTING?


A sauƙaƙe, Cloud Computing yana nufin amfani da kwamfuta da ajiya ta hanyar intanet, maimakon amfani da kayan aiki na hannu ko kwamfuta ɗaya kacal. Wato duk wani aiki ko bayanan da kake da su, maimakon ajiye su a cikin hard drive ɗin na'urarka, za ka iya ajiye su a "gajimare" (cloud) domin samun su daga ko ina a duniya.


YADDA CLOUD COMPUTING YAKE AIKI


Cloud computing yana aiki ne ta hanyar (servers) da ke ajiye bayanai a cibiyoyi na musamman. Wadannan bayanai za ka iya samun su ta amfani da na’urarka kamar waya, kwamfuta ko tablet – muddin kana da haɗin intanet.


Misalan Aikace-aikacen Cloud A RAYUWARMU:


1. Google Drive - iCloud - OneDrive – Domin ajiya da saukar da takardu, hotuna, da bidiyo.

2. Email Services (Gmail, Outlook, Yahoo) – Duk sakonnin email ana ajiye su a cloud.

3. Netflix, YouTube, Spotify– Aikace-aikacen da ke rarraba bidiyo da sauti daga cloud.

4. Selar.com -- Amazon KDP -- Canva – Masu rubutu da masu zane na amfani da cloud wajen aiki da adanawa.


FA'IDODIN AMFANI DA CLOUD COMPUTING:

-Ajiyar bayanai (Storage): Babu damuwa da rasa bayanai idan na’ura ta lalace.

- Aiki daga ko ina: Duk inda kake, zaka iya samun bayananka.

- Tsaro: Kamfanonin cloud suna da matakan kariya ga bayanan masu amfani.

- Saukin rabawa: Zaka iya rabawa da abokai ko abokan aiki cikin sauƙi.

- Sauƙin aiki tare (Collaboration): Mutane da dama na iya aiki a kan abu guda lokaci ɗaya.


MAFI SHAHARARRUN CLOUD SERVICES:


SUNA ---AIKI -----FREE STORAGE 

-Google Drive-- Takardu, hotuna, videos --15GB         

--iCloud --Apple devices --- 5GB          

--Dropbox --File sharing & storage --2GB         

--OneDrive -- Microsoft cloud service -- 5GB     


SHIN CLOUD COMPUTING ZAI AMFANE KA?


Idan kai ɗalibi ne, mai rubutu, mai kasuwanci, ko ma wanda ke ajiye hotuna da bayanai a waya – to tabbas cloud computing zai amfaneka. Zai baka dama ka guji asarar bayanai da samun dama da sauƙin aiki ko’ina.


KAMMALAWA


Cloud Computing ba kawai fasaha bace – wani salo ne na rayuwa a wannan zamani. Yana sauƙaƙa aiki, rage asara, da kuma ƙara haɗin kai. Idan har kana neman hanyar zamani ta adanawa da aiki cikin sauƙi, to lokaci yayi da zaka rungumi amfani da cloud.


Kuyi follow din Facebook page din mu 

https://www.facebook.com/share/1Jmzf5zmjH/

Comments

Popular posts from this blog

CONTENT CREATION (BLOGGING, YOUTUBE, SUBSTACK): CIKAKKEN BAYANI

BANBANCIN LAPTOP COMPUTER DA MINICOMPUTER

MENENE STRONG PASSWORD DA MISALI